--
Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu

Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu


Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kashe wasu gagararrun yan fashi da makami guda biyar a jihar Akwa Ibom 


Yan fashin, a cewar rundunar yan sandan, sun kware a satar mota da sayarwa a jihohin Akwa Ibom da Cross Rivers - C.P Ameingheme Andrew ya gargadi yan kungiyar asiri, 



fashi da makami, fyade da sauran miyagun laifuka, da su gaggauta kauracewa jihar Rundunar 'yan sanda ta jihar Akwa Ibom ta ce ta samu nasarar kashe yan fashi da makami shida wadanda suka kware a satar mota da sayarwa a jihohin Akwa Ibom da Cross Rivers.


Kwamishin 'yan sanda na jihar, Mr. Ameingheme Andrew a ranar Juma'a a Uyo, yayin holen gawar 'yan fashin ya ce an kashe su ne yayin bata kashi a kan hanyar Calabar zuwa Itu.


Ya bayyana cewa yan fashin suna kan hanyar su ta zuwa sayar da wata motar sata kirar Toyota Camry da suka sata a hannun wani likita da ke zama a Calabar, inda dubunsu ta cika. 


Kwamishinan wanda ya kama aiki kwanaki kadan da suka wuce, ya ce matattun yan fashin har sun tuntubi wanda za su sayarwa motar satar. 


Ya kara bayyana cewa rundunar 'yan sandan ta afke wani kasurgumin mai yiwa mata fyade, ta kuma cafke wani da ake zargin sa da kisan kan wani yaro mai shekaru 11. 


Haka zalika rundunar ta samu nasarar cafke 'yan kungiyar asiri guda biyar, da kuma wasu yan fashi da makami guda shida. 


"A yau, da misalin karfe 5:30 na safiya, mun samu kwakkwaran rahoto akan wasu yan fashi da makami guda shida, akan hanyarsu ta sayar da motar sata. 


"Da ma sun dade da addabar jihohin Akwa Ibom da Cross River, amma cikin nasara, bayan musayar wuta da jami'an rundunarmu, mun kashe su a hanyar Calabar zuwa Itu." 


Kwamishinan ya gargadi yan ta'adda da ke a cikin kungiyar asiri, fashi da makami, fyade da sauran miyagun laifuka, da su kauracewa jihar, ko su dandani kudarsu a hannunsa. 


Ya yabawa gwamnatin jihar da kuma al'umar Akwa Ibom akan goyon bayan da suka baiwa rundunar 'yan sanda a kokarinta na aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyanta. 


Dr. Arinze Obinna, mamallakin motar da yan fashin ke shirin sayarwa, ya ce sun tsare shi da bindiga yayin da ya ke kan hanyar komawa gida, inda suka kwace motar. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 


0 Response to "Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?