--
Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS

Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS


Wani jami’in dan sandan tafi-da-gidanka ya yi kira ga ruguza rundunar SARS - Jami’in da ke zanga-zanga ya ce jami’an SARS sun kama dan uwansa 


Yan Najeriya a fadin kasar na kira ga dakatar da rundunar SARS Wani mutum da aka ce jami’in dan sandan tafi-da-gidanka ne ya shiga sahun masu zanga-zanar neman a ruguza rundunar yan sandan SARS. 


Wani bidiyo da ya billo a yanar gizo ya nuno wani mutum sanye da rigar shan iska na rundunar yan sandan Najeriya sannan yana tattaki tare da masu zanga-zangar neman a ruguza sashin yan sandan SARS, jaridar The Cable ta ruwaito. 


Ya bayyana cewa ya biya wasu kudade domin ganin an saki dan uwnsa wanda jami’an SARS suka kama. Mutumin ya ce: 


“Sun kama dan uwana...ni da nake jami’in dan sanda, kun san nawa na biya? Allah ya hukunta su.”



A baya mun ji cewa fadar shugaban kasa tace an sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zanga-zangar da matasa ke yi saboda kashe-kashen da jami'an SARS ke yi. 


Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa akan harkokin watsa labarai ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba, matasa na tsaka da zanga-zanga akan kisan wulakanci da 'yan sanda ke yi. Yace Sifeta janar na 'yan sanda, Muhammed Adamu ya sanar da shugaban kasar a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba. 


Ahmed yace shugaban kasa zai tabbatar ya dauki mataki akai, kuma zai sauyasu da wasu 'yan sandan, yadda zai faranta wa 'yan Najeriya. Hadimin Buharin ya ce 'yan Najeriya suna da damar bayyanar da damuwarsu idan har shugabanninsu sun yi ba daidai ba. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?