Da duminsa: An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau
Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.
Sakon da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Twitter, ya ce "Gwamnatin jihar kaduna ta sanar da nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.
Ya maye gurbin Mai Martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, bayan ya kwashe shekara 45 yana kan mulki."
KADUNA UPDATE: The Kaduna State Government has announced the appointment of Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli as the 19th Emir of Zazzau. He succeeds HRH Alh. (Dr.) Shehu Idris who died on Sunday, 20th September 2020, after reigning for 45 years. pic.twitter.com/Wmmvhi1ifw
— Governor Kaduna (@GovKaduna) October 7, 2020
"Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920," a cewar sanarwar.
Latsa Nan Kukaranta Tarihin sabon Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli
Source: Bbc Hausa
0 Response to "Da duminsa: An naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?