
Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki a kan kawo karshen SARS - Kamar yadda takardar da aka fitar bayan taron ta bayyana, kwamitin fadar shugaban kasa ta amince da bukatu 5 na masu zanga-zangar
Sun bukaci a daina amfani da hukumar wurin tsayar da zanga-zangar kuma a saki dukkan wadanda aka kama Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya shugabanci taron masu ruwa da tsaki a kan tabbatar da bukatar kwamitin fadar shugaban kasa a kan gyara tsarin 'yan sanda.
Kamar yadda takardar wacce aka fitar bayan taron ta bayyana, masu ruwa da tsakin sun amince da bukatar masu zanga-zangar wanda ya hada da hana amfani da jami'an tsaro wurin dakatar da zanga-zanga tare da sakin wadanda aka kama.
Taron wanda ofishin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya tare da hukumar kula da hakkin dan Adam suka shirya, ya samu halartar shugabanni da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu, masu rajin kare hakkin dan Adam da sauransu.
Ma'aikatar kula da ayyukan 'yan sanda ta halarci taron inda ta tabbatar da cewa bukatu biyar na masu zanga-zangar sun dace a duba kuma gwamnati ta shawo kansu.
Source: Legit
0 Response to "Da duminsa: Kwamitin fadar shugaban kasa ya amince da bukatu 5 na masu zanga-zanga "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?