
Da duminsa: An kama mutum 30 yayinda ake zanga-zangar juyin-juya-hali a Lagas
Thursday, 1 October 2020
Comment
Suna adawa da manufofin gwamnatin Muhammadu Buhari wanda suka ce ya sanya al'umman kasar a cikin mawuyacin hali Daruruwan masu zanga-zanga a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, sun mamaye unguwannin jihar Lagas domin nuna rashin jin dadinsu a kan tabarbarewar shugabanci a Najeriya.
Masu zanga-zangan sun yi tattaki daga unguwannin Ojota zuwa Maryland a Lagas. An gano su suna wake-wake. Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kama masu zanga-zangar akalla su 30. Gamayyar masu zanga-zangar na juyin-juya hali a cikin wata sanarwa da suka saki kafin zanga-zangar, sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus.
Jawabin ya zo kamar haka: “Kungiyar juyin juya hali na kira ga dukkanin yan Najeriya a gida da waje da su fito kwansu da kwarkwata a ranar 1 ga watan Oktoba, domin shiga sahun zanga-zangar lumana da za a yi don neman a janye manufofin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kuntatawa mutane.
“Wadannan manufofi masu tsanani da suka sanya takunkumi a aljihun mutanen Najeriya na zuwa ne a lokacin da yan kasar ke farfadowa daga matsin annobar korona, lamarin da ya taba duniya baki daya, wanda kuma gwamnatin Buhari bata yi wa riko mai kyau ba, inda a yanzu ake sake fadawa matsalolin kudi. "
A wani labarin, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki. Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.
Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai. Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.
Source: legit.ng
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI:
0 Response to "Da duminsa: An kama mutum 30 yayinda ake zanga-zangar juyin-juya-hali a Lagas"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?