
Da duminsa: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar bude makarantun jihar
Kwamishinonin ilimi na jihohin arewacin Najeriya 19 sun amince cewa za a bude makarantun sakandire da firamare kafin ranar 31 ga watan Oktoba
Jihohin Bauchi, Neja, da Yobe sun sanar da ranakun bude makarantun sakandire da firamare
Sai dai, har yanzu babu sanarwa daga ma'aikatar ilimi ta tarayya da jihohi dangane da ranar bude makarantun gaba da sakandire
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za a bude makarantu ma su zaman kansu da na gwamnati a ranar 11 ga watan Oktoba domin fara zangon karatu na uku a kakar 2019/2020.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Kiru, ne ya sanar da hakan yayin taro da manema labarai ranar Alhamis a ofishinsa.
Kiru ya shaidawa manema labarai cewa gwamnati ta yanke shawarar bude makarantu bayan kammala taro da ma su ruwa da tsaki da kuma biyo bayan taron kwamishinonin ilimi na jihohin arewa 19 da aka yi a Abuja.
A cewar kwamishinan, ana umartar dukkan malaman makaranta su koma bakin aikinsu a ranar 11 ga watan Oktoba.
Source: Legit.ng
0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar bude makarantun jihar "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?