![Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi5bETXpt01kC5clF9Fcb2sd2DSKvNpj_oVeoF1FXsgxdS6FcIJQUXdagauC2WsRO4vimodLO7sadTJkbOvKpBjbhtxh2ToSW0e2b6hB7Y3YgI17-plnVOQ1w_4yonntCQsWD5Cu_x-enU/s320/a947126665a572bd.webp)
Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya soke zaben farko da masu zaben sarkin Zazzau suka yi - A yanzu haka masu zaben na gudanar da sabon nazari kan dukkanin yan takara 13 da suka nuna ra'ayin son zama Sarkin Zazzau na gaba
Hakazalika an mayar da yan takara biyu da aka cire a baya Tsarin zaben Sarkin Zazzau na 19 ya dauki sabon salo a ranar Laraba, 30 ga watan Satumba. A yanzu haka masu zaben Sarki a masarautar Zazzau na kan sabon matakin zabe, kamar yadda babban sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal ya bayyana.
Balarabe ya yi bayanin cewa gwamnan ya yi umurnin sake sabon zagaye na zabe bayan ya soke na farkon da aka yi, inda aka cire yan takara biyu.
Gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na twitter cewa: “A yanzu haka masu zaben sarki sun hadu don sake sabon nazari kan dukkanin yan takara 13 da suka nuna ra’ayinsu kan kujerar daga dukkanin gidajen sarauta, ciki harda mutane biyu da aka cire a baya. Za' a gabatar da rahoton nasu ga gwamna domin dubawa.
“A yanzu haka, masu zaben sarki na masarautar Zazzau na gudanar da sabon nazari don zabo wanda za a nada cikin masu takarar da zai zama Sarkin Masarautar Fulani ta Zazzau na 19. ''Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin yin sabon zagaye na zaben bayan da ta soke na farko da aka fara, inda aka cire yan takara biyu."
Muyiwa Adeleye, mai ba Gwamnan jihar shawara a kafofin watsa labarai, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa daya daga cikin yan takarar, Bunu Zazzau ya yi korafin cewa bai samu damar gabatar da takardar takararsa ba:
“saboda an fada masa cewa an rufe karba. “Hakazalika, Sarkin Dajin Zazzau ma ya yi zanga-zanga a kan cire shi da aka yi daga tsarin. An kuma lura cewa masu zaben Sarkin sun tantance yan takara biyu a ranar 24 ga watan Satumba, 2020, ba tare da sun ga takardunsu ba wanda aka karba a washegari.”
KADUNA UPDATE: The kingmakers are now meeting to assess all the 13 candidates that indicated interest from all the ruling houses, including the two that were previously excluded. The report of these assessments will be swiftly submitted to the governor for his consideration https://t.co/VIEwgoUci2 pic.twitter.com/s5xdOm3io7
— Governor Kaduna (@GovKaduna) September 30, 2020
Kingmakers of Zazzau Emirate are currently engaged in a fresh process to recommend candidates for the office of the 19th Fulani Emir of Zazzau. KDSG directed a new round of the selection process after cancelling the initial process, which excluded two interested applicants.
— Governor Kaduna (@GovKaduna) September 30, 2020
Source: Legit.ng
0 Response to "Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?