
Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan
Wasu matasa da ake zargin bata-gari ne sun banka wa ofishin 'yan sanda wuta a Ibadan - Hakan ta faru ne bayan 'yan sandan sun yi yunkurin tarwatsa masu zanga-zanga
Basu tsaya a nan ba, sun banka wa dukkan ababen hawan da ke farfajiyar ofishin wuta Wasu fusatattun matasa a garin Ibadan da ke jihar Oyo, sun banka wa ofishin 'yan sanda da ke Ojoo wuta. Ganau ba jiyau ba sun sanar da The Cable cewa rikicin ya fara ne bayan 'yan sanda sun yi yunkurin watsa masu zanga-zanga.
Wasu da ake zargin 'yan daba ne a cikin gayyar masu zanga-zangar sun dinga jifan 'yan sandan da duwatsu wanda hakan yasa 'yan sandan suka bude wuta. Fusatattun masu zanga-zangar sun fi 'yan sandan yawa kuma sun shige cikin ofishin inda suka banka masa wuta.
Da yawa daga cikin ababen hawan da ke farfajiyar ofishin 'yan sanda an kone su.
Karin bayani na nan tafe...
Source: Legit
0 Response to "Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?