Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe
Jama'a sun dinga neman inda za su boye domin ceton rayukansu a wurin tattar sakamakon zabe - Hakan ta faru ne sakamakon musayar ruwan wuta da ake yi tsakanin 'yan sanda da 'yan daba
An ji 'yan sandan suna shawarta jama'a da su san inda dare yayi musu sannan suna kokarin bai wa wurin tattara sakamakon kariya
Manema labarai, wakilan jam'iyyu da kuma masu lura da zabe sun tarwatse inda suka dinga neman maboya sakamakon ruwan wutar da ake musaya tsakanin 'yan sanda da 'yan daba.
Lamarin ya faru ne a makarantar firamare ta St Peter da ke Akure a ranar Asabar.
Ana amfani da makarantar firamaren wurin tattara sakamakon zaben karamar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar Ondo. Jami'an hukumar zabe suna ta hada-hada domin fara tattara sakamakon zabe a lokacin da rikicin ya barke.
"Ku bar nan, ku tafi! Bai kamata ku tsaya ba," wasu 'yan sanda ke sanar da hakan ga manema labarai da masu lura da zabe yayin da suke mamaye kofar shiga wurin tattara sakamakon.
Karin bayani yana nan tafe...
Source: Legit
0 Response to "Da duminsa: Ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan daba a wurin tattara sakamakon zabe"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?