
Da asusun bankunan fastoci muke amfani don guje wa jami'an tsaro - Dan damfarar yanar gizo
Wani dan damfarar yanar gizo yace suna amfani da asusun bankunan Fastoci idan suna jiran makudan kudi
Yace idan 'yan sanda suka kamasu, suna basu kudade masu tsoka don su rufa musu asiri Ya kara da cewa, ba su kadai suke damfara ba, har manya masu iyali suna fakewa da siyasa suna damfara Wani dan damfarar yanar gizo dake Warri, jihar Delta yace yana amfani da asusun bankunan mutanen kirki wurin adana kudaden damfarar da yayi saboda tsoron hukuma.
John ya ce idan yana jiran wani kudi mai yawa, wanda zai janyo zargin hukuma, yana neman Fastoci su ara mishi asusun bankunan su ya ajiye. Dan damfarar ya ce, sanin cewa kudade masu kauri suna shiga asusun bankunan Fastoci, ya tabbatar ba za'a zarge su ba.
A yadda jaridar Vanguard ta tattauna da dan damfarar, ya ce wasu Fastocin basu amince wa. A cewar sa, "muna samun Fastoci muyi ciniki da su, idan muna jiran kudade masu yawa, don gudun idon hukuma ya dawo kan mu, sai mu sa kudin a asusun bankunan su."
Ba'a cika zargi ba, komin yawan kudin da zai shiga asusun bankunan Fastoci. Ya kara da cewa, "yan sandan jihar Delta na samun kudi sosai a hannunmu, musamman yan sandan kan hanya." "Idan kuwa suka ga hoton turawa a wayoyin mu kuma suka fara zargi, ciniki mukeyi dasu," ya ce wasu suna bukatar N200,000 kafin su barmu mu tafi.
Da aka tambayeshi yadda suke biyan 'yan sandan, ce wa yayi, yawancin 'yan sandan suna nemo lambar asusun bankunan wadanda basu da wani hadi dasu ne, sai mu tura musu kudin. Da aka tambayeshi meyasa basa kai karar yan sandan, ce wa yayi, masu kudin halas ne suke kai kara, misali idan inada N2,000,000 a asusun bankina, ya za'ayi inkai kara? Ya ce,
"idan mukayi kokarin shiga Keke Napep don kada 'yan sanda su gane mu, suna tsayar da Napep din kuma su fito damu, don sun sanmu sosai. "Wannan shiyasa idan muka ga mun kusa isa wurin yan sandan kan titi muke fita da gudu, sai mu wuche 'yan sandan a kasa, Allah barshi idan sun gama duba Napep din sai mu shiga a can gaba dasu."
Ya ce har manya masu shekaru 40 zuwa 50 da 'yan kai, suna harkar damfarar yanar gizo. Ya ce zaka ga mutumin kirki da iyalansa, amma sana'arsa kenan. Wasu suna fakewa da siyasa, kuma ko ofishi basu da shi, amma suna rayuwa cikin wadata. Ya ce wasu 'yan damfarar siyasa ne.
Source: Legit.ng
0 Response to "Da asusun bankunan fastoci muke amfani don guje wa jami'an tsaro - Dan damfarar yanar gizo "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?