--
Bukin Maulud: Saƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo

Bukin Maulud: Saƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo


Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya aika sakon Maulidi ga Musulman jihar - Obaseki ya bukaci Musulman da su zamo masu aiki da koyarwar Annabi Muhammadu 


A yau Alhamis, 29 ga watan Oktoba ne al'umman Musulmi ke bikin zagayowar ranar haihuwar fiayyen halitta Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya taya al’umman Musulmi a jiharsa murnar zagaowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). 


Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen manzon tsira. Gwamnan ya yi wannan kira ne a cikin jawabin maulidin Annabi da ya ke gudana a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, jaridar Aminiya ta ruwaito. 



Obaseki ya ce, “Ina taya Musulmai maza da mata na jihar Edo da ma kasa baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.


 “A wannan rana muna kira da Musulmai mu ci gaba da nuna kauna da zaman lafiya, domin cigaban jiharmu da kasa baki daya”, inji shi. Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da zama makwabta nagari kamar yadda yake a koyarwar Ma’aikin.


Daga karshe ya yi kiran samun hadin kan mutanen jihar domin wanzuwar zaman lafiya. A gefe guda, yayin da musulman Najeriya ke farin cikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen annabi Muhammadu (SAW). 


Su nuna kauna da fahimta ga al'umma, da kuma bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa, Premium Times. 


A wani sako da shugaban kasa ya tura wa musulmai a kan maulidin fiyayyen halitta, wacce ta zama ranar hutu a Najeriya, ya roki 'yan Najeriya musamman matasa da su bar duk wani mummunan kudiri a kan zanga-zangar da ke jawo sace-sace da lalata dukiyoyi. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bukin Maulud: Saƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?