Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Isa Dutse
Wednesday, 7 October 2020
Comment
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban asibitin koyarwa ta Aminu Kano, Faresa Isa Dutse
Shugaban kasar ya ce rasuwar Farfesa Isa Dutse babban rashi ne ga fanin likitanci da Najeriya musamman a lokaci irin na yanzu da ake bukatarsa
Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin ya saka masa da gidan aljanna ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa
Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bakin cikinsa bisa rasuwar Farfesa Abdulahamin Dutse, tsohon shugaban Asibitin Koyarwa Ta Aminu Kano, inda ya ce mutuwarsa "babban rashi ne ga bangaren likitanci."
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin sakon ta'aziyya da ta fito daga bakin kakakinsa Garba Shehu a ranar Laraba a Abuja.
A cewarsa, rasuwar Farfesa Dutse ya tauye wa Najeriya daya daga cikin manyan likitocin da suka sadaukar da kansu wurin aikinsu. Ya kara da cewa an rasa marigayin ne a lokacin da kasar ke bukatarsa sosai sannan ya ce za ayi kewarsa.
Ya ce: "Daga abinda abokan aikinsa da dalibansa ke fada a kansa bayan rasuwarsa, Isa Dutse tabbas mutum ne da ya bada gudunmawa sosai a fanin likitanci, Najeriya da al'umma baki daya. "A matsayinsa na tsohon shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano, marigayi Farfesa Isa Dutse ya bar halaye na gari da zai zama abin koyi da na baya gare shi da abokan aikinsa.
"Ina son yi amfani da wannan daman don mika ta'aziyya ta ga Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, gwamnatin jihar Jigawa da Kungiyar Likitoci ta Najeriya bisa rasuwar fitaccen likita. "Da fatan Allah ya yi masa gafara ya saka masa da aljanna."
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sabunta wa'addin shugaban Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria na tsawon shekaru hudu. Sakatariyar dindindin na Ma'aikatar Sufuri, Dakta Magdalene Ajani ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwar da ta raba wa manema labarai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Source: Legit.ng
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Buhari ya yi alhinin mutuwar Farfesa Isa Dutse"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?