![Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi8RBrFaWYMCG6VHM5vU1hEVCEN3crkwslitmvmEu17KEBvk_vYT8oYd_rEKVLJljjo0Cv7zfu4QNXosYf4WoPFT2lxAMclZQjTKYfmSURMZ_CcH4wno0GONWUcnulxTufUb2MPiCuQ0kg/s320/814d979860ee4e63.jpg)
Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta
Friday, 2 October 2020
Comment
Wata budurwa ta yi wa saurayi wankin babban bargo sakamakon kyautar da ya bata na bikin zagayowar ranar haihuwarta - Budurwa Tola ta caccaki saurayinta mai suna Babatunde bayan ya tura mata N15,000 a matsayin kyautarsa
Ta bukaci kada ya sake kiranta har gaba da abada saboda ya kasance makwado wanda bai san darajar mace ba Wata hira tsakanin budurwa da saurayi ta bazu a kafafen sada zumutar zamani wacce ta janyo tsokaci kala-kala daga jama'a, shafin Linda Ikeji ya wallafa hakan.
kamar yadda hirar ta nuna, budurwar ta yi wa saurayin wankin babban bargo a kan kyautar da ya bata domin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta. Kamar yadda hirar ta nuna, budurwa Tola ta caccaki saurayinta mai suna Babatunde, bayan da ya yi mata murnar zagayowar ranar haihuwarta kuma ya tura mata N15,000.
Tola ta matukar tunzura a kan kyautar dubu goma sha biyar da ya bata kuma hakan yasa ta yi masa kaca-kaca tare da jan kunnensa da kada ya sake tuntubarta har abada. Ta zargi Babatunde da zama namiji makwado kuma wanda bai san darajar mace ba.
A wallafarta a shafinta na Twitter mai suna @adannanwaokolo, ta lissafa irin namijin da take so kuma ya miko kokon bararsa. Daya daga cikin yanayin mijin da take so shine ya kasance yana zama a tsibirin Legas, anguwar masu kudi ba ta talakawa ba.
"Barkanku, ni da kawata muna bukatar samari. Dole ne ya zama dogo, baki, mai aiki mai kyau, gwarzo a gado, yana zama a tsibirin Legas ba unguwar talakawa ba, mai gemu, mai kawatacciyar murmushi, mai shekaru daga 25 zuwa 30,"
ta wallafa. Adanna ta bayyana cewa, dole ta sa ta fito ta yi wannan tallar saboda "A rashin tayi a kan bar arha."
Source: Legit.ng
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI:
0 Response to "Budurwa ta yi wa saurayi kaca-kaca a kan bata N15,000 na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?