
Bidiyon basarake mai shekaru 82 yana cashewa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa
Alaafin na jihar Oyo ya cika shekaru 82 a duniya a ranar 15 Oktoban 2020. - Matansa sun hada mishi shagalin biki tare da taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Daya cikin matansa, Olori Memunat ce ta wallafa bidiyon shagalin a shafinta na Instagram Daya daga cikin manyan sarakunan kasar nan, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya cika shekaru 82 a duniya kuma daya daga cikin matansa ta shirya masa shagali.
Baya ga murnar, matansa sun shirya masa gagarumar liyafa. Bidiyon liyafar ya karade kafafen sada zumuntar zamani. Daya daga cikin matansa, Olori Memunat ce ta wallafa bidiyon basaraken yana rawa a liyafar. Duk da yawan shekarunsa, babu shakka zai iya fito-na-fito da matasa wurin iya rawa.
A cikin bidiyon, an ga kek na liyafar tare da kyaututtuka da ya samu daga masoya. Babu shakka basaraken yayi murnar liyafar da matansa suka hada masa. Ba a nan Olori Memunat ta tsaya ba, ta yi wata wallafa inda tayi bayanin cewa babu shakka za su iya yin komai don dauwamar da farin ciki a zuciyarsa. Ta yi wa sauran matansa jinjina. A kalamanta:
"Duk daya muke. Ba za mu iya yin komai ba amma za mu iya yin wani abu tunda Allah ya bamu iko. Ba za mu yi kasa a guiwa ba wurin saka shi farin ciki. Jinjina gareku sauran sarauniyoyi."
Kalli Bidiyon Anan:
Source: Legit
0 Response to "Bidiyon basarake mai shekaru 82 yana cashewa a bikin zagayowar ranar haihuwarsa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?