Bidiyo da Hotunan yanda akewa tsaffin mutane Fitsari a jiki da cin zarafi da sunan Maita a jihar Naija
Bidiyo da hotuna masu daga hankali sun watsu a shafukan sada zumunta inds aka ga wani mutum me suna Malam Hassan Patigi, dake ikirarin warkar da mayu yana cin zarafin wasu tsaffi ana musu fitsari a jiki da sunan mayune su.
An watsa hotunan sosai a shafukan sada zumunta inda hakan ya jawo caccaka. Lamarin ya farune a garin Mokwa dake jihar ta Naija. A wasu lokutan ana wa mutane tsirara saboda zargin maitar.
Kuma an zargi basaraken garin, Ndalilen Mokwa, Shaba Aliyu Muhammad da goyon bayan wannan lamari, kamar yanda wata kungiya dake yaki da cin zarafin mutane da sunan Mayu ta AFAW ta i zargi.
Shugaban kungiyar, Leo Igwe ya bayyana cewa ko kadan hakan bai dace ba dan cin zarafine da wulakanta da adam. An ga wata tsohuwa ana cin zarafinta a wajan da aka tara wasu mutane suna kallo.
Hakanan an ga wani tsoho ana mai fitsari a jiki. Igwe yayi kira ga gwamnatin jihar Naija da hukumar ‘yansanda dasu yi magana dan hana wannan lamari.
Kalli bidiyon lamarin:
Source: Hutudole
0 Response to "Bidiyo da Hotunan yanda akewa tsaffin mutane Fitsari a jiki da cin zarafi da sunan Maita a jihar Naija"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?