--
Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure

Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure


Bidiyon wata mata 'yar Los Vegas ya karade shafukan sada zumuntar zamani, inda aka ga matar cikin shiga irin ta amare - Matar ta biyo saurayinta har wurin aikinsa, tare da kawayenta da Fasto don a daura mata aure dashi take yanke 


A Bidiyon, ta nuna masa cewa matsawar yaki amincewa da tayin aurenta, to tabbas zata barshi har abada Hankula sun karkata akan bidiyon wata mata da tayi shiga irin ta amare a Los Vegas. A gefenta akwai kawayenta wadanda suka yi ado da wasu suturu masu kalar ruwan kasa, da takalma masu tsayi. 



View this post on Instagram

Getting married by fire, by force.

A post shared by Urban News (@urbannews254) on



Matar, wadda ba'a bayyana sunanta ba ta matsa cewa sai ta ga saurayinta dake aiki a wani shago. Tare da matar akwai Fasto, kuma tana rike da zoben daurin aure. Matar bata bukatar jin kalmar "a'a" daga bakin saurayin nata. 


An nuna matar tana fuskantar saurayin nata, inda tace indai har yaki amincewa da tayin aurenta to tabbas zata rabu dashi. Matar ta shayar da mutane da dama mamaki, a yadda ta dage kuma da alamun ta gama auna komai. Saurayin yayi mamakin al'amarin, inda ya daura kansa akan cinyarsa saboda tsananin mamaki. 



Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bidiyo da hotunan budurwa ta garzaya wurin aikin saurayinta cikin shigar amare, ta bukaci a daura musu aure "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?