Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki
Karfin hali ya kai wani matashi mai suna Kabiru shiga majalisar dokoki sata - Bai sani ba ashe na'urar CCTV na daukansa yayinda yake satan
Tuni an damke shi kuma an sanar da jami'an tsaron majalisar dokokin dake Abuja Wani matashi mai suna Kabiru a ranar Juma'a ya fasa cikin majalisar dokokin tarayya inda ya shiga ofishin wani dan majalisar wakilai ya kwashe daloli da wasu kayayyaki.
Wannan abu ya faru misalin karfe 2:30 na rana inda matashin yayi amfani wani mukulli na daban. An yi zargin Kabiru da kwashe daloli da kayayykin ofis irinsu na'urar kwamfuta, na'urar fotocofi da printer. SaharaReporters ta tattaro cewa Kabiru ya kasance hadimi ga wani dan majalisa daga Adamawa kuma sannanen mutum ne a majalisar.
Jami'an tsaron majalisar sun gane fuskarsa a bidiyon na'urar CCTV da ta daukeshi yana fashin. A yayinda ake tattara wannan rahoton, wasu yan majalisa wanda ya hada da mai magana da yawun mambobin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, na wajen da aka kama matashin.
An samu labarin cewa dan majalisar da matashin ke yiwa aiki yana kokarin ganin an yi rufa-rufa kawai a manta da lamarin. Bidiyon na'urar CCTV ya nuna matashin lokacin da yake satan.
Source: Legit.ng
0 Response to "Barawo ya fasa cikin majalisar wakilai, ya kwashe daloli da kayayyaki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?