Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta
Dr Hakeem Baba-Ahmed, jigon APC a jihar Kaduna, yayi magana akan shigar diyar Ribadu ranar aurenta - Ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace shigarta ta sha banban da koyarwar addininta da kuma al'adarta
Ya kuma roki iyaye da kuma matasa da su daina kwaikwayon shigar yahudawa, wadda tayi karo da koyarwar Musulunci Dr Hakeem Baba-Ahmed, jigon APC a jihar Kaduna, yace shigar auren Fatima Ribadu tayi hannun riga da koyarwar addini da kuma al'adarta.
Idan baku manta ba, shagalin bikin Aliyu Abubakar dan mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da diyar tsohon shugaban EFCC da akayi a Asokoro, Abuja ranar Asabar. ya samu halartar manyan baki. Kyakyawar amaryar da ta gama Nigerian Turkish International College, dake Abuja a 2015, ta saka wata rigar amare wadda yanayin adonta na Dubai ne.
"Gabadaya bai dace da addini da kuma al'adarta ba," cewar Dr Hakeem Baba-Ahmed. Dr Hakeem ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Lahadi, inda yake rokon iyaye da kuma matasa musulmai akan daina kwaikwayon al'adun yahudawa.
Kamar yadda ya wallafa, "A yau ne naga hotunan bikin wata yarinya musulma, tayi shiga wadda ta saba da addini da kuma al'adar ta." Ya kara da cewa, "Irin haka yana tada min da hankali. Ina rokon iyaye da kuma matasa da su dena kwaikwayon al'adun da suka saba wa tamu."
Ya kuma roki masu bin shafinsa da kada suyi wani tsokaci na batanci a wallafar nan tasa ko kuma zagi. Wani Harun Elbinawi yayi nasa tsokacin, inda yace, "A arewacin Najeriya, ana amfani da dokar shari'a ne akan talakawa.
"Suna zartar da dokar shari'ar musulinci ne akan talakawan arewacin Najeriya amma babu mai sabawa dokoki da tsarin addini kamar su. "Sannan suna amfani da kalaman musulinci idan suna so su yaudari talakawa."
Source: Legit.ng
0 Response to "Bai dace da addini da dabi'a ba - Dr Hakeem ya caccaki shigar sirikar Atiku a ranar aurenta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?