--
Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki

Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki


A hira ta musamman, Saleh Mamman ya yi bayanin halin da lamarin wutan lantarki ke ciki - Ya ce gwamnati ta tsame hannunta daga cikin harkar wuta gaba daya 


Ya jaddada cewa babu yadda gwamnati ta iya kan lamarin karin farashin wuta Ministan wutan lantarki, Injiniya Saleh Mamman ya bayyana cewa babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji a bangaren wuta ba karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari. 


Buhari ya nada Saleh Mamman ministan lantarki baya nasara a zaben 2019. Ya gaji Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje na yanzu. A hirar da yayi da BBC Hausa, Saleh Mamman ya ce kashi 80 zuwa 90 na masu samun wutan lantarki zasu tabbatar an samu canji na wutan lantarki. Ya ce gaba daya Najeriya an samu karin wutan lantarki karkashin gwamnatin Buhari. 


Ya kara da cewa babu gari ko anguwar da zata ce ta kwana daya ba'a kawo wuta ba sai da idan wani abu ya lalace. Yace: "Kashi 90 ko 80 daga cikin yan Najeriya dake samun wutan lantarki, tsakani da Allah idan ka tambayesu ko akwai canji, wallahi zai fada maka akwai canji." 


"Babu gari ko wani gefe a kasar nan wanda zai ce maka an wuni tun daga safe har dare ba'a kawo mashi wuta ba, da sharadi guda, sai dai akwai matsala. Wakil taransfoman unguwarsu ta samu matsala ko ta lalace." 


"Amma ina tabbatar maka cewa tun da muka kama ragamar mulki, babu garin da za'a waye gari tun daga safe har dare ba'a samu wuta." 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Babu dan Najeriyan da zai ce ba'a samu canji ba - Ministan Lantarki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?