--
An yi cacar baki tsakanin mawaki Wizkid da hadimar Buhari

An yi cacar baki tsakanin mawaki Wizkid da hadimar Buhari


Hadimar Buhari, Lauretta Onochie tayi cacar baki da wani fitaccen mawaki mai suna Wizkid, saboda ya kira Buhari da 'Tsoho' - Duk da kowa ya san Wizkid bai fiya yin tsokaci ko surutai marasa amfani ba a kafafen sada zumuntar zamani, sai gashi yayi a wannan karon 


Wizkid ya mayar mata da martani, inda yace mata taji kunya, a matsayin ta na mace kuma uwa, SARS na can suna kashe yaran mutane sunyi shiru Wata hadimar Buhari mai suna Lauretta Onochie ta caccaki fitaccen mawaki Wizkid akan ya kira shugaban kasa Buhari da 'Tsoho'. Mawakin bai yi kasa a guiwa ba, sai da ya mayar da martani ga hadimar shugaban kasan. 




 Wizkid, wanda aka san baya fitowa yana surutai da tsokaci marasa makama a kafafen sada zumuntar zamani, ya caccaki Buhari bayan shugaban kasar yayi wa shugaban kasar Amurika fatan samun lafiya daga cutar coronavirus da ya kamu da ita. Mawakin ya jefi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kalmar 'tsoho'. 



View this post on Instagram

The Next Level begins today!

A post shared by Muhammadu Buhari (@muhammadubuhari) on


Onochie tayi wa mawakin kaca-kaca, inda tace mishi bashi da daraja na gaba dashi kuma yarinta na damunsa, shiyasa ya jefi Buhari kalamar nan. Mawakin ya ce, Mai shekaru 77 dai ba yaro bane. Ya ce ita kanta Onochie tana da yara, kuma bata damu da yadda SARS ke kashe 'ya'yan wasu ba. 



Wizkid yace shima uba ne, kuma ba shekaru ne ke sa mutum yayi mulkin kasa yadda ya dace ba. Ya ce da Onochie ya kamata taji kunyar furta kalaman ta. Ga dai yadda ya wallafa: "Mai shekaru 77 fa ba yaro bane, tsoho ne. 


Kuma ke mace ce, kuma uwa. 'Yan sanda na can suna kashe yaran mutane amma kun kasa magana. Gaskiya kunji kunya!!! Kunji kunya!!! Ni uba ne, kuma na tabbatar da cewa ba shekaru bane kesa mutum yayi mulki na kwarai." 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "An yi cacar baki tsakanin mawaki Wizkid da hadimar Buhari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?