--
An sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

An sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kafin Soli a Katsina sun sace matar mai gidan biredi - Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin 


Ana zargin 'yan bindigan sun kai harin ne saboda bayanan sirri da mazauna kauyen ke bawa jami'an tsaro Gungun 'ƴan bindiga sun mamaye ƙauyen Kafin Soli da ke ƙaramar hukumar Kankiya a jihar Katsina 


inda suka ɗauke matar sanannen mai gidan burodi a yankin, Ahmed Muhammad. Muhammad shine mamallakin gidan burodin Safiya (Safiya Bread) a ƙauyen Kafin Soli. 

Mazauna yankin sun shaidawa masu rahotanni cewa 'ƴan bindigar sun mamaye ƙauyen tun karfe 12 na dare inda suka shafe awa uku suna gudanar da ayyukan su kafin daga bisani su sace amaryar zuwa inda ba'a sani ba a kan babura. 

Wani mazaunin ƙauyen ya shaidawa 'ƴan jarida cewa ana zargin 'ƴan bindigar sun zo ramuyar gayya ne sakamakon kama masu kai musu bayanai da jami'an tsaro suka yi. 


"Sun kawo harin ramuyar gayya ne saboda basu ji daɗin yadda aka tona asirin masu basu bayanai a gun jami'an tsaro ba wanda hakan yayi sanadiyyar kama masu basu bayanan,"a cewarsa. 


Ya kuma ƙara da cewa wata ƙila jami'an tsaro sun yi amfani da na'urar bin diddigi don gano masu basu bayanan a kusa da rugar da ke gab da ƙauyen. 


Yace 'ƴan bindigar sun kawo hari aƙalla sau biyar kauyen sakamakon bayanan da suke samu daga masu basu bayanan. Mai magana da yawun 'ƴan sanda jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace hukumar 'ƴan sanda tana gudanar da bincike don tabbatar da sun gano masu laifin domin su gurfanar dasu a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "An sace amaryar mai gidan burodi a Katsina"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?