An Kashe Matashi Saboda Budurwa A Kano
Sunday, 4 October 2020
Comment
Al’ummar Unguwar Sheka a Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano sun wayi gari da alhinin mutuwar wani dan unguwar, Sagir Muhammad wanda aka zargi matashi Abdullahi Muhammad da kashewa.
Ana zargin Abdullahi ya kashe Sagir Muhammad xan kimanin shekara 22 ta hanyar dukansa, saboda samun sabani da suka yi a kan wata budurwa.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa rigima ce ta auku a tsakanin matasan biyu a kan wata budurwa da ke unguwar.
Majiyar ta ce bayan da lamarin ya faru an garzaya da marigayin wata karamar cibiyar lafiya da ke unguwar ta Sheka inda kuma a nan ne rai ya yi halinsa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike a kai
Source: Aminiya Daily Trust
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "An Kashe Matashi Saboda Budurwa A Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?