--
An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu

An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu





An gano wani lauyan bogi a yayin da ya tafi kotu domin kare wani mutum a jihar Ogun - Alkalin kotun bai gamsu da wasu abubuwa da lauyan ya yi bane yasa ya tambaye shi shekarar da ya samu izinin fara aikin lauya 


Da ya bincika bai ga sunan lauyan bogin ba hakan yasa ya kira 'yan sanda suka tisa keyarsa zuwa caji ofis 'Yan sandan jihar Ogun sun kama wani lauyan bogi Tajudeen Idris mai shekaru 47 kan zarginsa da yin soja gona. 


An kama wanda ake zargin ne a ranar Juma'a a kotun Majistare ta 6 da ke karamar hukumar Ifo na jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito. 


An ruwaito cewa Idris ya hallarci kotun ne gaban mai shari'a I.A. Arogundade domin kare wani Ifeanyi Chukwu da ke shari'a da Ayo Itori. 


Ya yi ikirarin cewa shi lauya ne da ke aiki da Tajudeen O. Idris & Co. Chambers kuma ya hallarci kotun ne don kare daya daga cikin wadanda ake yin shari'a da shi. Kakakin 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin. 


Oyeyemi ya ce yanayin yadda lauyan bogin ya gabatar da kansa a kotun ne yasa aka fara zargin ko tabbas shi lauya ne. Hakan yasa alkalin kotun ya tambaye shi shekarar da ya samu izinin fara aiki a matsayin lauya kuma ya ce 2009. 


"Amma binciken da aka yi ya nuna babu sunansa cikin wadanda suka samu izinin aikin lauya a shekarar 2009 hakan yasa aka gayyaci 'yan sanda. "DPO na 'yan sanda na yankin Ifo, CSP Adeniyi Adekunle ya tura jami'ansa suka kama wanda ake zargin inda yanzu ake cigaba da bincike a kan lamarin." inji shi. 


A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki. Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "An kama lauyan bogi yana tsakar kare wani a kotu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?