An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno
Jami'an hukumar tsaro na NSCDC sunyi nasarar cafke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan sakon 'yan ta'adda ne
An kama mutanen hudu Usman Baptel, Alphonsus John, Nicholas Benjamin da Isaac Clement bisa zargin samarwa 'yan ta'addan man fetur
An kama su ne dauke da jarkokin man fetur 34 shake da man fetur da suka boye cikin buhunna a kan babura
Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Borno ta kama mutane hudu da ake zargin 'yan sakon 'yan kungiyar Boko Haram ne da jarkoki 34 na man fetur.
Daily Trust ta ruwaito cewa kwamandan hukumar na jihar, Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da wadanda ake zargin a ranar Juma'a a Maiduguri.
Abdullahi ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin, Usman Baptel shine manajan wani gidan mai a kauyen Husara da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno
Ya ce sauran sun hada da Alphonsus John, Nicholas Benjamin da Isaac Clement da aka kama a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Wastilla da ke karamar hukumar Michika da ke jihar Adamawa da ke makwabtaka da Borno.
Yace kayan da aka kama su da shi sun hada da jarkokin man fetur masu lauyin ruwan dorawa dauke da fetur kimanin lita 880 da aka boye su cikin buhunna a kan babura uku.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama wadanda ake zargi da laifi 1,318 a wannan shekarar.
An gama bincike kan 734 yayin da saura 468 ana kan bincikarsu kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.
Source: Legit.ng
0 Response to "An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?