--
Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa

Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa


Dan babban Malamin addinin Musuluci ya rasu ahadarin mota ranar Asabar - Manyan malamai a fadin Najeriya sun aika sakon ta'azziyarsu ga iyalansa Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! Allah ya yiwa AbdulMalik, 'dan gidan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam rasuwa ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2020. 


Legit Hausa ta samu labarin daga wajen ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim ali Pantami, Sheikh Abdullahi Umar Gadon Kaya da Sheik Dr Mansur Sokoto ta shafukansu na Facebook. A cewar Minista Pantami, " 


Na samu labarin rasuwar AbdulMalik, 'dan Shaykh Ja'afar Mahmud Adam (RH). Ina mika ta'aziyya zuwa ga yan'uwansa da iyayensa, kan Allah Ya jikansa, Ya jikan iyayenmu da sauran yan'uwanmu, kuma Ya kyautata namu bayan na su,... 


"Wanda ya mutu, bai yi sauri ba. Mu da muke nan bamu dade ba, sai mun zo"... in sha Allah" A cewar Dr Mansur Sokoto, matashi AbdulMalik ya rasu ne sakamakon hadarin mota. "Yanzu muke smaun labarin mun rasa danmu Abdulmalik Jafar Mahmud Adam cikin wani hatsarin mota, " cewar Dr Sokoto. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?