Aliyu Soba: ALGON ta tsige mataimakin shugabanta na ƙasa, ta naɗa sabo
Thursday, 8 October 2020
Comment
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa, ta maye gurbinsa da wani sabo.
Kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa, Aliyu Soba an maye gurbinsa da Jega Shehu - Kakakin kungiyar, Obiora Orji ya sanar da cewa an tsige ne saboda ya karya wasu dokokin da kungiyar
A bangarensa, Soba ya ce ba a sanar da shi batun tsige shi ba kuma ba a bashi dama ya kare kansa ba idan ana tuhumar da wani abu Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.
Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar. Sanarwar da Kakakin ALGON, Obiora Orji ya bawa kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Laraba a Abuja ya nuna ƙungiyar ta zaɓi Jega Shehu ya maye gurbin Soba.
Orji ya ce dukkan ƴan Majalisar Zartarwa na Ƙungiyar da Kwamitin Amintattu sun amince da tsige Soba a taron da suka yi a ranar Laraba a Asaba, jihar Delta. Ya ce an tsige Soba ne saboda saɓa wasu dokoki na kundin tsarin kungiyar ta ALGON.
A bangarensa, Soba ya ce bai da masaniya kan batun tsige shi yayin hirar wayar tarho da ya yi da wakilin NAN
Ya bayyana tsigewar da aka ce an masa a matsayin abin zargin don ba su da ikon tsige shi. "Zaɓe na aka yi don haka idan za a tsige ni sai a bi dokokin da ke kundin tsarin mulkin jam'iyya. "Idan har za a kira taron NEC a tsige ni tabbas akwai dalili kuma ban san dalilin ba. "Kafin a tsige ni, ya dace a bani damar kare kaina kan zargin da ake min.
"Idan akwai wani zargi da aka yi wa ofishi na, kamata ya yi su sanar da ni sai in kare kai na," a cewar Soba. Mista Soba ya ƙara da cewa idan an sanar da shi cewa an tsige shi a hukumance, zai sanar da matsayin sa da na kungiyar reshen jihar sa.
Source: Legit.ng
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Aliyu Soba: ALGON ta tsige mataimakin shugabanta na ƙasa, ta naɗa sabo"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?