Akalla mutane 36 ne suka mutu yayin da wasu 470 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa A Jihar Sokoto
Thursday, 8 October 2020
Comment
Mutane Akalla 36 ne suka mutu yayin da wasu 470 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa A Jihar Sokoto
Mista Mustapha Umar, Daraktan Agaji da Wayar da kai na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakoto (SEMA) shine ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a ranar Alhamis a Sakoto.
A cewarsa, Ambaliyar ruwan ta lalata gonaki da kayan gona masu dumbin yawa tare da Kashe shanu da su ka kai a kalla 120 a fadin jihar.
Haka zalika ya bayyana cewa, kananan hukumomi 19 ne a cikin 23 Ambaliyar ta shafa tun farkon fara damunar a wannan shekara ta 2020.
Hakanan, Shugaban Hukumar ta NEMA dake jihar Sokoto, Dakta Kofoworola Soleye , wanda ya wakilci Darakta Janar, AVM Muhammadu Muhammed (mai ritaya) ya ce an yi taron ne da nufin tattaunawa tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki kan abin da ya shafi Annobar da kuma yadda za a bullo da hanyoyin tunkarar lamarin.
Source:Hutudole
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Akalla mutane 36 ne suka mutu yayin da wasu 470 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa A Jihar Sokoto"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?