--
'Abun ya fi karfina' - Sanwo-Olu ya magantu a kan kaiwa ma su zanga-zanga hari a Lekki Toll Gate

'Abun ya fi karfina' - Sanwo-Olu ya magantu a kan kaiwa ma su zanga-zanga hari a Lekki Toll Gate


Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bawa al'ummar jiharsa hakuri game da harbe-harben da jami'an tsaro suka yi a Lekki Toll Gate 


Gwamnan ya ce lamarin ya sha karfinsa ne amma ya yi alkawarin zai yi aiki tare da gwamnatin tarayya don shawo kan lamarin 


Sanwo-Olu ya yi wannan jawabin ne bayan ziyartar wadanda suka jikkata inda ya yi alkawarin gwamnati za ta basu kulawa da ya dace 


Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas ya dora laifin kan 'wasu abubuwa da suka fi karfinsa' a yayin da ya ke tsokaci kan harin da aka kai wa masu zanga-zangar #EndSARS a jiharsa. 


A ranar Talata, jami'an tsaro sun yi harbi a lokacin da suke kokarin tarwatsa masu zanga-zanga a Lekki Toll gate a Legas inda wasu da dama suka samu rauni kuma ana fargaba wasu sun mutu. Lamarin ya janyo maganganu a cikin kasar har ma da kasashen waje.


A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Sanwo-Olu ya ce zai tabbatar duk wadanda suka samu rauni sun samu kulawa a asibiti kuma yana aiki da gwamnatin taraya don gano ainihin abinda ya faru. "Wannan shi ne dare mafi muni a rayuwarmu ganin wasu abubuwa da suka fi karfinmu aikata munanan abu a tarihinmu, amma zamu shawo kan lamarin tare", a cewar gwamnan.


"Yanzun nan na kamalla ziyarar asibiti don duba wanda harbe-harben ya rutsa da su a Lekki. "Na dauki lokaci kafin gabatar da jawabi saboda lafiyar al'ummar da abin ya shafa ne ya fi abinda ya fi muhimmanci a wuri na. 


"Yanzu haka akwai marasa lafiya 10 a babban asibiti, 11 a asibitin Redington sai 4 a asibitin Vedic; wanda kanana da matsakaitan raunika sai kuma 2 da suke karbar kulawa ta musamman.


"An sallami marasa lafiya uku kuma zamu ci gaba da bibiyar halin da suke ciki da kuma tabbatar da dukkanin marasa lafiya sun samo kyakkwawar kulawa. 


"A matsayina na gwamnan jiharmu, na san nauyin abinda ya faru da kai na kuma zanyi aiki da gwamnatin tarayya don tabbatar da an shawo kan wannan matsalar da kuma daidaita ayyukan jami'an tsaro don kula da lafiya da dokiyoyin al'ummar jihar." Sanwo-Olu ya saka dokar ta baci tsawon awa ashirin da hudu, saboda tashe tashen hankula a jahar. 




 


 Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "'Abun ya fi karfina' - Sanwo-Olu ya magantu a kan kaiwa ma su zanga-zanga hari a Lekki Toll Gate "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?