--
 Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo da za'ayi gobe Asabar

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo da za'ayi gobe Asabar


Shirye-shirye na cigaba da gudana na zaben gwamnan jihar Ondo da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta shirya ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2020. 


Tuni hukumar ta fara raba kayayyakin zabe masu muhimmanci irinsu na'urar tantance masu zabe wanda akafi sani da 'Card Reader, takardun kuri'a da akwatunan zabe zuwa dukkan lunguna da sakon jihar Ondo.


Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, tare da shugabannin kwamitin zaman lafiya ta kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, AbdulSalam Abubakar, sun tabbatar da cewa dukkan yan takara sun rattafa hannu kan takardan alkawarin cewa ba zasu yi rigima ba. 


Legit Hausa ta kawo muku sharhin abubuwa bakwai da ya kamata ku sani game da zaben gwamnan kamar yadda taswirar TheCableIndex ya nuna: 


1. Adadin yan takara: Yan takara 17 zasu kara a zaben gobe. Yayinda 16 maza ne, akwai mace guda daya kacal 


2. Adadin kananan hukumomin da za'ayi zabe a jihar: Akwai kananan hukumomin 18 a jihar Ondo kuma ana kan tura kayayyakin zabe yanzu haka, kamar yadda INEC ta bayyana. 


Kananan hukumomin sune Akoko North-East, Akoko North-West, Akoko South-East, Akoko South-West, Akure North, Akure South, Ese Odo, Idanre, Ifedore, Ilaje , da Ile Oluji/Okeigbo. Sauran sune, Irele , Odigbo , Okitipupa, Ondo East, Ondo West, Ose da Owo. 


3. Adadin gundumam dake jihar: Akwai gunduma-gunduma 203 a fadin jihar Ondo


4. Adadin rumfunan zabe. Akwai rumfar zaben 3009 


5. Adadin mutanen da ake kyautata zaton zasu kada kuria: Mutane 1,478,460 suka karbi katin zabensu. 


6. Adadin katin zaben da ba'a karba ba: Kimanin mutane 343,886 basu karbi ktin zabensu ba kuma ba zasu iya kada kuri'a ba. 


7. Su waye manyan yan takara?: Akwai manyan yan takara uku cikin yan takara 17, sune: Oluwarotimi Akeredolu SAN - Jam'iyyar APC Eyitayo Jegede SAN - Jam'iyyar PDP Agboola Ajayi - Jam'iyyar ZLP




Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to " Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da zaben gwamnan jihar Ondo da za'ayi gobe Asabar "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?