
Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarki, bari in karanta tarihin nadin sarki a Zazzau - El-Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna na shirye-shiryen zabawa masarautar Zazzau mai tarihi sabon sarki - El-Rufa'i na bayyana cewa duniya ta zuba ido kan wanda zai zaba
Ya yi addu'a Allah ya bawa masu zaben sarki a masarautar hikiman zaben na kwarai Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana wani abin birgewa da yakeyi domin wayar da kasan kafin yiwa masarautar Zazzau zaben sabon sarki bayan rasuwar marigayi Shehu Idris.
Da yammacin Alhamis, gwamna El-Rufa'i ya daura hoton wani littafin tarihi da aka wallafa kan masarautar Zazzau da yadda aka zabi sarakuna a baya.
Littafin wanda bature, M.G Smith, ya wallafa mai suna 'Government in Zazzau' na dauke da yadda salon mulkin masarautar tsakanin shekarar 1800-1950.
El-Rufa'i ya ce yana sake karanta littafin ne domin kara ilimi kafin ya yanke shawara kan wanda zai zaba.
El-Rufai yace: "Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarkin masarautar Zazzau, ina sake karanta littafin Farfesa G Smith kan yadda akayi zaben sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 da zai daura ni kan hanyar zaben na kwarai)."
KADUNA UPDATE: While awaiting the recommendations of the Zazzau Emirate kingmakers, I am re-reading Prof M G Smith’s authoritative epic on the selection of Zazzau Emirs from 1800 to 1950 to guide me in taking a decision. “Government in Zazzau” was published in 1960. - @elrufai pic.twitter.com/h4sgPlUvXw
— Nasir Ahmad El-Rufai (@elrufai) September 2Rariyamm0
Source: Legit.ng
DAGA:
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL:
0 Response to "Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarki, bari in karanta tarihin nadin sarki a Zazzau - El-Rufa'i "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?