
Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo
Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya lashe zaben gwamnan jihar Edo na 2020 - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tabbatar da nasarar Obaseki bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben -
Babban abokin hammayarsa, Fasto Ize-Iyamu na jam'iyyar All Progressive Congress, APC, ne ya zo na biyu a zaben Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tabbatar da Mista Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Edo a karo na biyu bayan ya yi nasarar doke abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC.
Wannan shine karo na biyu da Obaseki ke yin nasara a kan Ize-Iyamu, inda a shekarar 2016 ma hakan ta kasance sai dai a lokacin Obaseki ya yi takara a karkashin APC yayin da Ize-Iyamu ke PDP.
INEC ta sanar da cewa Obaseki ya zama zakara ne a zaben gwamnan bayan samun kuri'u mafi rinjaye na 307,955 inda mai biye masa Ize-Iyamu ya samu kuri'u 223,619.
Wanda ya zo na uku a zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP da kuri'u 323, sai na hudu dan takatar jam'iyyar LP da ya samu kuri'u 267.
Hukumar zaben ta ce adadin masu zabe da aka tantance domin kada kuri'a a jihar 557,443, yayin da adadin kuri'u masu sahihanci 537,407. Jimillar kuri'un da masu zabe suka kada 550,242, sannan kuri'un da suka lalace kuma 12,835.
Jam'iyyu 14 ne suka gabatar da 'yan takara a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020.
Source: Legit.ng
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Yanzu-yanzu: INEC ta sanar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?