
Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar cike sabon fom din banki
Gwamnatin Tarayya ta bawa 'yan Najeriya hakuri bisa sakon da ta fitar a jiya Alhamis na cewa masu asusun bankuna su tafi banki su cike wani fom na musamman
Gwamnatin ta ce an fitar da sakon ne a kan kuskure kuma ba batu ne da ya shafi kowa ba sai dai wani rukunin mutane da galibinsu ba 'yan kasa bane da masu wasu irin kasuwannci na musamman
Sanarwar da gwamnatin ta fitar a jiya Alhamis ya fusata 'yan Najeriya da dama inda suka yi ta nuna bacin ransu a dandalin sada zumunta Gwamnatin Tarayyar Najeriya, FG, ta nemi afuwar 'yan kasar kan sanarwar da ta fotar na cewa dukkan masu asusun ajiyar kudi na banki su tafi bankunsu su karbi fom din kai-da-kai da za su cike.
A baya Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin tarayyar ta fitar da sanarwa ta shafin ta na Twitter cewa dukkan masu asusun banki har ma da kamfanonin inshora za su cike wasu fom inda za su bayar da wasu bayannai a kansu.
Gwamnati ta bada umurnin ne a ranar Alhamis duk da cewa masu asusun bankuna suna da lambar tantacewa na bankuna wato BVN da ke kunshe da muhimman bayanansu da kuma lambar dan kasa wato NIN.
Sanawar ya ce ya yi baranazar cewa duk wanda bai tafi ya cike fom din ba zai iya fuskantar hukunci da ya hada ta rufe masa asusun banki ko kuma cin sa tara.
Wannan sanarwar da gwamnatin ta bada ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta inda mutane da dama suka nuna rashin jin dadinsu game da batun da suke ganin kawai wahal da su za ayayi,
We apologize for the misleading tweets (now deleted) that went up yesterday, regarding the completion of self-certification forms by Reportable Persons. The message contained in the @firsNigeria Notice does not apply to everybody. FIRS will issue appropriate clarification shortly pic.twitter.com/KBiPh0lCwJ
— Government of Nigeria (@NigeriaGov) September 18, 2020
Sai dai a ranar Juma'a gwamnatin ta fitar da wani sabon sanarwa inda ta nemi afuwar 'yan kasar a kan sanarwar da ta ce mai rikitarwa ne.
"Muna neman afuwa bisa ga sakonnin da muka fitar a jiya game da batun cike fom. Sanarwar ba kowa ta shafa ba. Hukumar tattara haraji @firsNigeria za ta yi karin bayani nan gaba."
A sakon da FIRS ta fitar, ta ce wasu rukunin mutane ne kawai za su cike wannan fom din. Mutanen galibi ba 'yan kasa bane da kuma wasu da ke kasuwannci da suke biya wa haraji a sassan kasar daban-daban.
Source: Legit
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Yanzu-yanzu: FG ta nemi afuwar 'yan Najeriya kan sanarwar cike sabon fom din banki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?