
Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu
Mambobin jam'iyyar SPN tare da wasu sauran matasa a jihar Legas sun shirya zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin mai da wutar lantarki
Sai dai, jami'an 'yan sanda sun tarwatsa gungun matasan tare da kama wasu daga cikin jagororin zanga-zangar
Har yanzu 'yan Najeriya a fusace suke da gwamnati saboda karin wutar lantarki da farashin litar mai Jami'an rundunar 'yan sanda sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur.
An kama masu zanga-zangar ne a yau, Alhamis, a yankin Ojuelegba da ke garin Legas. Jaridar Punch ta rawaito cewa bayan masu zanga-zangar da aka kama, an kwace kayan aikin 'yan jaridu. Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, Hassan Soweto, ya ce an kama mutane 18 da suka hada da 'yan jarida.
"An kama mu tare da 'yan jarida da mambobin jam'iyyar SPN da safiyar yau (Alhamis) yayin da muka fito zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki.
"A yanzu haka da nake rubuta wannan sako ina kulle a bayan motar 'yan sanda a hanyar zuwa hedikwatarsu," a cewar Soweto, shugaban matasan SPN.
A wani labarin, hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da 'Kwastam' ta samu rabanu na biliyan ₦976.6 daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2020.
A wata takarda da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa ranar Alhamis, an nuna cewa an samu kudaden ne daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu Najeriya da kudin duti da sauransu. NAN ta bayyana cewa takardar ta fito ne daga ofishin hulda da jama'a na hukumar kwastam.
Kididdiga ta nuna cewa kudaden da hukumar Kwastam ta samu daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu basu taba kaiwa yawan na wannan karon ba. Alkaluma sun nuna cewa kudaden haraji da aka kara a kan kaya (VAT) sune ke bin bayan yawan kudin da hukumar ta samu daga rabanu a kan shigo da kaya.
Source: Legit.ng
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu; 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama wasu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?