
'Yan sanda sun cafke makusancin Gwamna Yari yana taron sirri da 'yan bindiga a Zamfara
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta cafke wani makusancin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari a garin Gusau
An gano cewa, an cafke Dan-Tabawa sakamakon kama shi da aka yi da wasu 'yan bindiga 17 suna taron sirri
Amma an gano cewa, bayan amsa tambayoyi da yake a hannun 'yan sanda, akwai umarnin da ya zo daga Abuja a kan cewa a sake sa Jami'an 'yan sanda a jihar Zamfara sun damke wani mutum mai suna Abu Dan-Tabawa,
makusancin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, bayan da yake taron sirri da wasu wadanda ake zargin 'yan bindiga ne a Gusau, babban birnin jihar. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an kama Dan-Tabawa ne bayan rahoton da aka samu daga na'urar nadar hoto da Gwamna Bello Matawalle ya saka a dukkan fadin babban birnin Gusau.
An gano cewa, a halin yanzu Dan-Tabawa yana amsa tambayoyi a hannun 'yan sandan jihar. Daily Nigerian ta wallafa cewa, rundunar 'yan sandan na kokarin sakin wanda ake zargin sakamakon wani umarni da ake zargin ya zo daga Abuja.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya tabbatar da cewa Dan-Tabawa ya shiga hannun jami'an tsaron tare da wasu mutum 17 da ake zargi. Kakakin rundunar 'yan sandan, a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce kamen bashi da wata alaka da siyasa.
Ya ce: "Kamen ya samo asali ne daga bayanan sirrin da aka samu kuma rundunar 'yan sandan tana yin iyakar kokarina wurin ganin cewa ba a yi karantsaye ga zaman lafiya ba a jihar. "An yi kamen ne domin bai wa dukkan jama'ar jihar da yankin baki daya tsaro.
"Rundunar tana sanar da dukkan jama'ar jihar da su guji fadawa cikin kowanne al'amari da zai zama kalubale ga tsaro, komai kuwa girma ko darajar su."
Source: Legit.ng
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "'Yan sanda sun cafke makusancin Gwamna Yari yana taron sirri da 'yan bindiga a Zamfara "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?