--
Shugabancin kasa a 2023: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo

Shugabancin kasa a 2023: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo


Batun wa zai mulka Najeriya bayan saukar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza akala - Wata kungiyar Yarabawa, IPSC tayi kira akan a bar ibo su mulka Najeriya a 2023 


Kungiyar tace mulkin Najeriya a hannun ibo zai kawo adalci, hadin kai da kuma ba wa kowa hakkinsa Kungiyar Igbo for President Solidarity Congress (IPSC), wata kungiya ce a kudu maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da bada hadin kai dari bisa dari akan shugabancin dan kudu maso gabas a shekarar 2023. 


Ta ce yin hakan ne kadai zai kawo hadin kai a Najeriya. Shugaban kungiyar, Dr Olukayode OshinAriyo ne yayi wannan kiran a ranar Talata, 29 ga watan Satumba a Ibadan, jihar Oyo. IPSC ta ce kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna, 


kudu maso gabas suna da damar rike kujerar shugabancin kasar Najeriya. Kungiyar tace ayi amfani da NC na 2014, wanda yace kowanne dan kasa zai mulkar Najeriya. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 


 

Related Posts

0 Response to "Shugabancin kasa a 2023: Yarbawa sun juya wa Tinubu baya, suna goyon bayan Ibo "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?