
NUC Ta Umarci Jami’o’i Su Fara Shirin Budewa
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya (NUC) ta umarci dukkannin jami’o’i da su fara shirye-shirye nan take domin ci gaba da karatu baya rufe sakamakon bullar cutar COVID-19.
Sanarwar da NUC ta aike wa Shugabannin Jami’o’i ta ce hakan na zuwa ne duba da raguwar masu cutar da bullarta ta sa aka rufe makarantun a a ranar 23 ga watan Maris, 2020.
“Sakamakon jawabin Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da COVID-19 cewa an samu raguwar masu cutar sosai, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da bukatar NUC na cewa jami’o’i su fara shirye-shirye nan take domin ci gaba da harkokin karatu”, inji sanarar.
Ka’idojin bude jami’o’i
Sai dai hukumar ta gindaya sharudda biyar da ya wajaba kowace jami’a ta cika kafin a bude ta domin gaba da karatu.
Dole a kiyaye matakan kariyar da tsare-tsaren Hukumar Yaki da Cutttuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) na hana yaduwar cutar.
Babu dalilin da zai sa a rusa tsarin zangon karatun NUC da ya danganci adadin kwanakin kowane zangon karatu.
Dole ne a tabbatar da kiyaye dukkannin dokoki da ka’idojin NUC na tabbatar da inganci.
NUC da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya za su kai ziyarar gani da ido domin tantance irin tsare-tsaren kare lafiya da ingancinsu a jami’o’i ta bangaren kayan aiki, dakunan karatu, ofisoshi, ajujuwa, dakunan kwanan dalibai, dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin kula da lafiya da sauransu.
Dole ne daga lokaci zuwa lokaci jami’o’in za su rika sanar da NUC game da halin da suke ciki.
Source: Aminiya Daily Trust
DAGA:
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL:
0 Response to "NUC Ta Umarci Jami’o’i Su Fara Shirin Budewa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?