--
Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait

Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait


Bayan rasuwar tsohon sarki Sheikh Sabah, Kuwait ta samu sabon sarki - An tattaro cewa Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Sarki 


Sheikh Nawaf ya sha alwashin yin aiki domin samar da daidaito da tsaro a Kuwait Rahotanni sun kawo cewa an nada Sabon Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah. 


Tuni dai sabon sarkin ya karbi rantsuwar kama aiki. Wannan ci gaban na zuwa ne kwana daya bayan sanar da rasuwar tsohon Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah. 


Sheikh Nawaf, wanda shi ne yarima mai jiran gado a baya, ya dauki alkawarin yin aiki domin samar da daidaito da tabbatar da tsaro a Kuwait. 


Ba a tsammanin Sheikh Nawaf mai shekara 83 zai kawar da kasar daga manufofin cikin gida da na ƙasashen duniya da magabacinsa kuma dan uwansa ya samar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito. 


A baya, mun kawo cewa Sarkin Kuwait mai shekaru 91 da haihuwa, Sarki Sabah Al-Ahmad Al-Sabah ya rasu ranar Talata a wani asibiti a Amurika. "Muna bakin cikin sanar da mutuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-jaber Al-Sabah, sarkin Kuwait," 


inji Sheikh Ali Jarrah Al-Sabah, ministan yada labaran kasar. An haifi Sheikh Sabah a shekarar 1929, ya rike kujerar ministan harkokin kasashen waje na tsawon shekaru 40, tsakanin 1963 zuwa 2003 daganan ya zama shugaban kasa. 


Ya zama sarkin Kuwait a watan Janairu, 2006 bayan rasuwar Sheikh Jabeer Al-Sabah. A watan Augusta 2019 an sanar da rashin lafiyarsa duk da ba'a fadi cutar da ke damunsa ba, har ta kai ga an kwantar da shi a asibiti. An fitar dashi Amurka don duba lafiyarsa a watan Yulin 2020. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

Related Posts

0 Response to "Kwana daya bayan rasuwar tsohon Sarki: An nada sabon Sarkin Kuwait "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?