--
Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata

Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata


Katsalandan daga bangaren wasu surukai na daga cikin abubuwan da ke haddasa mutuwar - Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ibadan ta raba auren shekara uku saboda irin wannan hali na shiga rayuwar ma'aurata 


Uwar Amarya ta yi zargin cewa uban Ango ya hana ma'aurata su yi rayuwarsu ta aure yadda suke so A ranar Talata ne wata kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Ile-Tuntun, jihar Oyo, ta raba wani auren shekara uku saboda katsalandan din uban miji a rayuwar auren dansa. 


Uwargida Ibukun Amosun ce ta shigar kara a gaban kotun domin neman ta raba aurenta da mijinta, Babatunde, saboda tsangwamar da ta ke sha a wurin mahaifinsa. A cewar Ibukun, surukinta ya gurbata zuciyar mijinta har ta kai ya yi watsi da al'amuranta.


Da ya ke zartar da hukunci a ranar Talata, alkalin kotun, Henry Agbaje, ya ce kotunsa ta raba auren ne domin a samu zaman lafiya. 


Kazalika, ya gargadi tsofin ma'auratan su guji bijiro da duk wani hali da kan iya haifar da sabuwar rigima a tsakaninsu. A cewar Ibukun, mazauniyar unguwar Apata a garin Ibadan, aurenta da Babatunde ya lalace ne saboda yawan tsangwamarta da mahaifinsa ke yi. 


"Ina da aikina mai kyau a Legas tun kafin na auri Babatunde Kuma mun kulla yarjejeniyar cewa zan cigaba da aiki bayan aurenmu. "Amma bayan mun yi aure sai ya sanar da ni cewa sai na bar aiki, na dawo gida na yi zaman aure, ni kuma na nuna rashin amincewata. 


"Haka na lallabashi har ya yarda ya barni na cigaba da aikina. Sai dai, hakan bai yi wa iyayensa dadi ba saboda duk lokacin da ya ziyarcesu sai ya sauya ra'ayi a kan maganar aikina. "Wataran bayan na dawo daga wurin aiki sai na iske an sauya makullin gida. 


Da na kirashi na tambayi dalili sai ya sanar da ni cewa mahaifinsa ne ya bashi shawarar ya yi hakan. "Bayan hakan, iyayensa sun yi watsi da yunkurin a sasantamu," kammar yadda Ibukun ta sanar da kotu. Mahaifin Babatunde ya musanta zargin cewa ya umarci dansa ya rufe gidansa don kar Ibukun ta sake shiga. 


"Mai girma mai Shari'a, ban umarceshi ya rufe mata gida ba, amma maganar gaskiya; ba zamu jurewa halayenta ba. "Mu a al'adarmu, dole miji da mata su zauna tare, amma mahaifiyarta ta goya mata baya wajen kin zama da mijinta da kuma daukan juna biyu. 


"Sannan ba ta shigar mutunci, ta na saka sutura kamar ba matar aure ba kuma haka ta ke fita babu ko kunya," a cewarsa. 


Babatunde bai halarci zaman kotun ba, mahaifinsa ne ya wakilce shi. A nata bangaren, mahaifiyar Ibukun ta zargi mahaifin Babatunde da hana ma'auratan su yi rayuwarsu yadda suke so. 


Source: Legit.ng

DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?