
Karin farashin wutar lantarki: Karuwai suna shirin fadawa yajin aiki
Wata kungiyar karuwai da ke Onitsha a jihar Anambra, ta bayyana damuwarta a kan karin farashin man fetur da wutar lantarki
Kamar yadda shugabar kungiyar wacce ta kira kanta da magajiyarsu tace, korona ta yi musu babbar illa sai kuma ga wannan - Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta dubesu
domin sun samu karin kudin haya da sufuri, hakan babbar illa ce garesu Karuwai da ke aiki a Onitsha, jihar Anambra, karkashin wata gagarumar kungiyarsu,
sun sha alwashin fadawa yajin aiki a kan tashin farashin man fetur da na wutar lantarki.
Daya daga cikin shugabanninsu mai suna Uto Nwanyi, wacce tace ita ce magajiya, ta jajanta yadda korona ta yi musu illa kuma karin farashin man fetur da wutar lantarki ya kara musu a kai.
"Matsalar korona ta fara a watan Maris na wannan shekarar, kuma ya dauka watanni hudu. A cikin wannan lokacin, bamu samun kwastomomi kuma bamu iya samun abubuwan bukatunmu.
“Bamu gama jin radadin korona ba sai gwamnatin tarayya ta kawo karin farashin man fetur da wutar lantarki.
"Hakan ya kawo karin kudin haya, sufuri da dukkan rayuwa. Hakan ta matukar matsanta wa duk wata kungiya a Najeriya. Muna kira ga gwamnati da ta janye wannan karin," tace.
Uto Nwanyi, wacce suka yi magana tare da wata abokiyar aikinta mai sunn Phina, ta ce idan hukumomi basu dauka mataki ba, ba su da wani abu da ya wuce su shiga yajin aiki.
A wani labari na daban, a ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, 2020, kungiyar ‘yan kwadago a Najeriya ta NLC ta ba gwamnati wa’adin janye karin da ta yi a kan kudin mai da wuta.
NLC ta ce za ta tafi yajin aiki muddin aka shafe makonni biyu daga yanzu ba tare da gwamnatin tarayya ta maida farashin man fetur da wuta kamar yadda su ke ba.
Kungiyar kwadagon ta ce takwarorinta za su jawo abubuwa su tsaya cak, idan wa’adin da su ka bada ya wuce ba tare da gwamnatin kasar ta lashe aman da ta yi ba.
Source: Legit ng
DAGA:
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL:
0 Response to "Karin farashin wutar lantarki: Karuwai suna shirin fadawa yajin aiki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?