
Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16
Wani sabon hoto na iyalan biloniya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya bayyana - An gano shahararren dan kasuwar zaune a tsakiyar yaran nasa su 16 wanda dukkansu mata ne Sarina dai shine shugaban rukunin kamfanonin Azman, wato kamfanin sufuri na Azman da na hada-hadar man fetur da gas da kuma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama
Kamar yadda kuka sani, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya kasance shahararren dan kasuwa Najeriya kuma yana cikin sahun farko na biloniya a kasar. Har ila yau Sarina ya kasance shugaban rukunin kamfanonin Azman, wato kamfanin sufuri na Azman da na hada-hadar man fetur da gas da kuma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Azman.
Baya ga arziki na kudi da Allah ya azurta dan kasuwar da shi, ya kuma azurta shi da haihuwar yaya da yawa. A bisa ga wani hoto shafin Instagram na ‘Arewa Heritage’ya wallafa, an gano mai rukunin kamfanonin na Azman tare da ahlinsa su goma sha shida, wadanda aka bayyana a matsayin yaransa mata.
A jikin hoton an wallafa rubutu kamar haka: “Ahlin Azman da mahaifinsu...Babban tawaga ke garemu.”
Source: legit.ng
0 Response to "Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?