
Kalli Hotunan fusataccen matashi mai digiri daya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta
Matashi Usman Abubakar dan asalin jihar Katsina, ya yayyaga takardun makarantarsa baki daya - Kamar yadda kafofin sada zumunta suka bayyana tare da hoton matashin, an tabbatar da cewa ya kammala hidimtawa kasa
Dalilinsa na yaga takardunsa dukkansu kuwa tare da banka musu wuta bai wuce fusatar da yayi saboda rashin aikin yi ba Hotunan fusataccen matashin da ya yayyaga takardun makarantarsa dukkansu ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.
Kamar yadda hotunan suka karade kafofin sada zumuntar zamani na Twitter da Facebook, an ga matashin ya yaga takardunsa sannan ya banka musu wuta.
An gano cewa, matashin dan asalin jihar Katsina ya kammala karatunsa har zuwa matakin digiri amma samun aiki ya gagara.
Matashin mai suna Usman Abubakar, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya bayyana, ya kammala hidimar kasarsa. Wasu jama'a sun alakanta halin da ya shiga da kasar nan yayin da wasu ke cewa gajen hakuri ne rashin hankali ya kai saurayin ga wannan aika-aikar.
Kalli Hotunan Takardun:
Source: Legit.ng
0 Response to "Kalli Hotunan fusataccen matashi mai digiri daya yaga takardun makarantarsa, ya banka musu wuta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?