
Kalli Hotuna: 'Yan sanda sun yi holen 'yan fashi da makami da masu garkuwa a Abuja
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi holen wasu da ake zargi da yan fashi da makami ne, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane - Cikin wadanda aka kama har da wasu da ake zargin sun kai wa motar kai kudi banki hari a Ebonyi sun kashe yan sanda
Rundunar 'yan sandan ta yi holen makamai, bindigu, alburusai, khakin sojoji da wasu kayayyakin da aka kama a hannunsu Rundunar 'yan sandan Najeriya a ranar Laraba 30 ga watan Satumba ta gabatar da wasu da ake zargi da aikata fashi da makami, garkuwa da 'yan bindiga da 'yan sanda na musamman masu yaki da 'yan fashi SARS suka kama a jihohi daban-daban.
Mutum bakwai da ake zargin suna da hannu cikin fashin da aka yi wa motar daukan kudi tare da kashe 'yan sanda a jihar Ebonyi a ranar 29 ga watan Yulin 2020 suna cikin wadanda aka yi holen su.
Shugaban tawagar, Sunday Shoyemi mai shekaru 46 ya ce kwana biyu suka yi suna shirin yadda za su kai harin amma rashin jituwa da suka samu a tsakaninsu ya janyo aka kama su. Shoyemi wanda a baya sana'ar kamun kifi ya ke yi ya ce ya yi nadamar abinda suka aikata kuma wannan ne fashin da ya yi na farko a rayuwarsa.
Wani daga cikin wadanda aka gabatar da su, John Nnoma mai shekaru 58 daga jihar Abia ya ce ya kan bada alburushi shi kuma a bashi namun daji.
Nnoma ya ce ya saba boye alburushin a cikin kayan gwanjo da ya kamata a siyar a Taraba shi kuma sai a biya shi da namun daji. Da ya ke yi wa manema labarai jawabi kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba ya ce:
"Duk yadda kake tunanin kana da dabaru, wata rana asirin ka zai tonu, kuma duk iya wayon ka, 'yan sanda za su kama ka." Makaman da aka kwato a hannunsu sun hada da harsasi, albursai, bindigu kirar AK 47, AK 49, GPMG, kudi Naira 258,570 da sabbin khakin sojoji guda 583.
A wani labarin, Rundunar 'yan sandan jihar Delta na neman tsohon karamin ministan ilimi, Kenneth Gbagi ruwa a jallo kan zargin cin zarafin wasu ma'aikatansa a Signatious Hotel.
Tunda farko Legit.ng ta ruwaito cewa Gbagi wanda shine mai otel din, wai ya bada umurnin da tube ma'aikatansa hudu, hudu mata da na miji daya a sannan aka dauki hotunansu da bidiyo aka baza a dandalin sada zumunta.
Source: Legit.ng
0 Response to "Kalli Hotuna: 'Yan sanda sun yi holen 'yan fashi da makami da masu garkuwa a Abuja"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?