
Rigar Kowa: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza
Gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau
Gwamnan ya bayyana cewa za a yi jana'izar basaraken da karfe 5 na yamma a garin Zazzau Ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na mika ta'aziyyarsa ga jama'ar Zazzau da jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya. Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi.
"Cike da alhini nake tabbatar da mutuwar baban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr, Shehu Idris Idris," El-Rufai ya wallafa a Facebook.
Ya kara da cewa, "Ya rasu a asibtin sojoji na 44 da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya. Za a yi jana'izarsa a garin Zazzau da karfe 5 Insha Allah.
"Za a kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a yayin jana'izar da karbar makokinsa. “Na sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban rashin kuma yana mika ta'aziyyarsa.
"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci wakilan gwamnatin tarayya zuwa Zaria domin ta'aziyyar mai martaba a masarautar Zazzau da jihar Kaduna.
“Mun rasa babban abun alfaharinmu, mai cike da hikima sannan uban kowa. Allah ya bashi masauki a Aljanna Firdau. Amin"
Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi. Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi. "Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.
"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar
Source: Legit.ng
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Rigar Kowa: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?