
Duba Kasashe 5 a fadin duniya masu matukar wuyar ziyarta da dalilin hakan
Sau da yawa ganin sunan kasa ko kyawawan hotunanta kan sa jama'a su ji sha'awar kai ziyara - Amma kuma ba kowacce kasa bace take maraba da baki ko son ganinsu baki daya
Dalilansu kan fara da rashin hatimin shiga kasa ko rashin jirgi kai tsaye har kasar Kafin ka fara tafiya zuwa wata kasa a fadin duniya, akwai matukar amfani idan ka gane cewa ba dukkan kasashen duniya bane suka maraba da kai ko kuma suke son ganinka.
A saboda haka, dole ne a bincika tare da gano kasashen da ke da wuyar zuwa ko kuma basu maraba da baki. Dalilansu sukan fara da rashin samun hatimin shiga kasar, rashin jirgi kai tsaye da zai kai ka da sauran dalilai.
1. Libya Da yawa daga jami'an gwamnati kan bada shawara tare da jan kunne a kan zuwa kasar Libya. Idan kana son shiga kasar, sai dai ta kasar Misra idan ba daga nahiyar Afrika bane.
Babu jirgi kai tsaye da ke kai mutum zuwa Libya daga Ingila ko Amurka, amma kamfanin jragen sama na Afriqyah yana zuwa daga Istanbul zuwa Tripole ko kuma daga Tunis.
2. North Korea Kasar North Korea bata maraba da baki, kuma za su yi komai da za su iya wurin ganin sun hana jama'a kai ziyara. Suna bukatar duk bako da ya biya kudin zagayen da zai yi a yayin ziyara. A yayin ziyarar, dole ka ksance tare da mai jagorar.
Rashin ofishin jakadancin kasar a kasashe masu yawa na duniya na nufin cewa sai dai a nemi damar shiga kasar ra China.
3. Turkmenistan Kafin aminta da shiga kasar Turkmenistan sai ka amince da dan jagora wanda hakan ke da matukar tsada.
4. Bhutan A kusan karni 50 da suka gabata, jama'a basu iya ziyartar masarautar Bhutan. A halin yanzu, akwai kamfanonin jiragen sama biyu da ke shige da fice a kasar. Amma kuma nan dole ne a samu dan jagora wanda dan asalin kasar.
5. Syria A halin yanzu ana tsaka da rikici a kasar Syria kuma basu bai wa kowa hatimin shiga kasarsu. Kowanne hatimin shiga kasar kan dauka dogon lokaci kafin a bada damar amfani da shi.. Sau da yawa a kan hana hatimin bayan dogon lokaci.
Source: Legit.ng
0 Response to "Duba Kasashe 5 a fadin duniya masu matukar wuyar ziyarta da dalilin hakan "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?