
Da duminsa: Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba
Bayan jita-jita da rade-radi, Minista Sadiya ta auri babban Sojan Najeriya - Majiyoyi sun bayyana cewa an yi daurin auren nan ranar Juma'a
A baya ana cewa shugaba Buhari ne ke shirin auren Sadiya Umar Farouq Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya auri Ministar walwala da jin dadin al’ummma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, Daily Trust ta ruwaito.
Majiyoyin daban-daban sun tabbatarwa Daily Trust cewa an yi daurin auren ne ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2020 a Masallacin Juma’an Maitama dake Abuja.
”Da gaske ne Shugaban Mayakan saman da ministar walwalar mutane sun yi aure,” daga cikin majiyoyin ya fada. “Mutane kalilan aka gayyata saboda ma’auratan da yan uwansu basu son a yada labarin,“
Wata majiyar tace sun dade suna soyayya. ”Sun kwana biyu suna soyayya amma abinda ya faru ranar Juma’a ya kawo karshen jita-jitan da akeyi cewa tana soyayya da shugaba Muhammad Buhari.” Tace
A bangare guda, Sama da daliban makaratun firamare milyan tara suke amfana da shirin ciyarwa da gwamnatin Buhari ke gudanarwa a fadin tarayya, ministar walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana.
Sadiya ta ce sama da masu girki dubu 100,000 aka dauka aiki domin girkawa daliban abinci a jihohi 34 a fadin tarayya kawo yanzu. Ministar ta bayyana hakan ne ranar Juma'a a taron murnar shekara daya da kafa ma'aikatar, Daily Trust ta ruwaito.
Ta kara da cewa kafa ma'aikatar ya rage matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa. A cewarta, kimanin matasan da suka amfana da shirin N-Power 109,823 suka kafa kasuwacin kansu a garuruwansu.
Source: Legit ng
DAGA:
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL:
0 Response to "Da duminsa: Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?