
Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo
Ana fargabar cewa an harbi wani mutum a wurin kada kuri'a a Ologbo a jihar Edo - Basaraken Ologbo, Jason Owen Akenzua ya tabbatar da cewa ya ji karar harbin bindiga
Akenzua ya kuma ce ya tuntubi DPO na 'yan sanda amma ya fada masa 'yan sanda ne suka yi harbin don tarwatsa mutane Rahotanni da ke fitowa daga karamar hukumar Ikpoba Okah na jihar Edo sun bayyana cewa an harbi wani mutum daya da bindiga a Ologbo.
Da aka tuntube shi game da harbin da aka ce an yi a Ologbo Dukedoom, Enogie, Mai martaba Jason Owen Akenzua ya ce ya ji karar harbin bindiga.
Amma untubi DPO na 'yan sanda an fada masa cewa 'yan sanda ne su kayi harbi a lokacin da wurin zaben ya rincabe. 'Na ji karar harbin bindiga kuma na kira DPO na Ologbo a waya.
Ya ce min 'yan sanda ne suka yi harbi don tarwatsa wasu mutane da ke neman tada hayaniya a wurin. Hankula sun kwanta a wurin yanzu." ya ce.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?