--
Babu gaskiya a ‘bidiyoyin’ nada Yariman Zazzau kan sarauta inji San Turaki

Babu gaskiya a ‘bidiyoyin’ nada Yariman Zazzau kan sarauta inji San Turaki


Yariman Zazzau ya musanya rade-radin cewa an nada shi sabon Sarki  Maniru Jafaru ya karyata wannan ne ta bakin San Turakin Zazzau jiya Jita-jita sun fara yawo a jiya Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2020, cewa an nada wanda zai gaji Marigayi Shehu Idris a kujerar Sarkin Zazzau. 


Rade-radin da ake yi shi ne Yariman Zazzau, Maniru Jafaru ne aka zaba a matsayin sabon Sarki. Sai dai San Turakin Zazzau, a madadin Yarima, ya fito ya karyata wadannan labarai da bidiyoyin bogi da su ke ta yawo tun ranar Lahadi da safe. 


San Turaki, Sirajuddeen Balarabe Yakubu ya fara jawabinsa ne da cewa: “Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.” 


“Ina so a madadin Yariman Zazzau, Hakimin Basawa, Maniru Jafaru in yi gajerar sanarwa.” “Ni Sirajuddeen Balarabe Yakubu, San Turakin Zazau, ina so in jawo hankalin jama’a, da fadar Sarki, da masoya cewa su yi watsi da labaran bogi da bidiyoyin da ke yawo a gari.” 


San Turakin Zazau ya ce, “Babu bukatar in maimaita abin da ya ke yawo a cikin wadannan bidiyo.” “Gwamnati da gwamnan jihar Kaduna gaba daya, ba su kai ga bada wata sanarwa game da nadin sabon sarkin Zazzau ba.


” Inji San Turaki. “Wasu ne da Allah kadai ya sansu da manufarsu, su ka kirkiri wannan labari da faifen bidiyoyi." 


“Mu na so mu yarda cewa an yi su ne da niyyar kirki, idan an yi ne domin a nuna goyon-baya, mun godewa haka.” Ya ce, amma duk da haka, mu na kira da a guji yin irin wadannan abubuwa, da San Turaki ya kira ba gaskiya ba, kuma labaran bogi. 


A karshe, Balarabe Yakubu, ya kara da kira da a cigaba da addu’a tukuru na ganin an zabi Sarki nagari wanda zai maye gurbin Shehu Idris. Idan za ku tuna, Shehu Idris ya rasu ne a ranar 20 ga watan Satumba, 2020. 


Kawo yanzu an shafe fiye da mako guda babu Sarki a masarautar Zazzau. Yayin da ake lissafin sabon Sarki, har kun ji cewa Hasken Fadar Kano ya tare a Zaria, ya na goyon bayan Ahmad Nuhu Bamalli daga gidan Mallawa 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Babu gaskiya a ‘bidiyoyin’ nada Yariman Zazzau kan sarauta inji San Turaki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?