
Babbar magana: Buhari ya yi amai ya lashe ana gobe bikin Nigeria @60
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amai ya lashe kan sanarwar da ya fitar ta yiwa 'yan Nigeria jawabi kai tsaye daga dandalin Eagle, Abuja
A cikin wata sabuwar sanarwa daga Mr Femi Adesina, shugaba Buhari, ya bukaci 'yan Nigeria da su yi watsi da waccan sanarwar ta baya
A sabuwar sanarwar da aka fitar yammacin ranar Laraba, Buhari ya ce zai gabatar da jawabi ga yan Nigeria ta talabijin da karfe 7 na safiyar ranar Alhamis A yammacin ranar Laraba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa ba zai gabatar da jawabi ga yan Nigeria a dandalin Eadle Square kamar yadda ya yi niyya a baya ba.
Haka zalika, shugaban kasar ya sanar da cewa, a yanzu zai gabatar da jawabin ne kai tsaye ga 'yan kasar ta talabijin daga fadar shugaban kasa.
Femi Adesina, babban hadiminsa ta fuskar watsa labarai, ya fitar da sanarwa kan cewar Buhari zai gabatar dan jawabin ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.
A cikin sabuwar sanarwar, Adesina ya bukaci 'yan Nigeria da su yi watsi da waccan sanarwar ta baya, wacce ta nuna shugaban kasar zai gabatar da jawabin kai tsaye daga Eagle Square, Abuja.
Haka zalika, ya bayyana cewa, da zaran shugaban kasar ya gama gabatar da jawabin na sa, zai wuce kai tsaye dandalin Eagle Swuare, wajen taron cikar Nigeria shekaru 60 da samun yanci.
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya maye gurbin wasu jakadun Nigeria guda biyu da ya kai sunansu gaban majalisar dattijai amma ba a tantance su, ya kawo sabbin mutane biyu.
Ya maye gurbin Peter Gana (Niger) da Muhammed Manta (Niger), sai kuma Yusuf Mohammed (Yobe) da Yusufu Yunusa (Yobe). Wannan sabon nadin na kunshe a cikin wata wasika da shugaban kasar ya aikewa shugaban majalisar dattijai, kuma Ahmad Lawan, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata.
Source: Legit.ng
0 Response to "Babbar magana: Buhari ya yi amai ya lashe ana gobe bikin Nigeria @60 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?