
Abin da ya sa za a rage cunkuso a gidajen yarin Najeriya
Gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara wani yunkuri don rage cunkoso a gidajen yari ta hanyar sakin kananan yaran da ke tsare a wannan lokaci na annobar korona da ma bayanta.
Ministan shari'ah na Nijeriya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka yayin wani taro ta intanet kan yin afuwa da rage cunkoson yaran da a ka hana wa 'yanci a ƙasar.
Tun farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya kafa kwamitin da zai duba yiwuwar rage cunkoson ƙananan yara a gidajen yarin ƙasar, da kuma yin gyaran fuska kan aikace-aikacen gidajen yarin.
Daga cikin wadanda za su ci gajiyar shirin sun haɗa da wadanda shekarun da a ka yanke musu tuni sun ci adadi mai yawa, da kuma matan da ke zaman gidan yari tare da 'ya'yansu da a ke tsoron za su iya kamuwa da cutar Korona.
Hakama za a saki wadanda ba su da lafiya, ko kuma su ke neman kulawa ta musamman daga likitoci saboda wasu cutuka da su ke dauke da su.
Shima shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa mai shari'a Ishaq Bello, ya ce aikin zai kasance wani jadawali na samar da wani tsari mai ɗorewa.
A na sa ran yawan ƙananan yaran da a ke tsare da su a gidajen yari a Najeriya ya ragu da kashi hamsin cikin dari bayan kammala shirin.
Source: Bbchausa
0 Response to "Abin da ya sa za a rage cunkuso a gidajen yarin Najeriya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?