Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta
Wednesday, 26 August 2020
Comment
Wata kotun Majistare da ke garin Osogbo, a jihar Osun, a ranar Talata ta bukaci a tsare mata wata matar aure mai shekaru 44 a duniya mai suna Adetoro Olawuni, a gidan gyaran hali.
Ana zargin Adetoro da watsa wa mijinta mai suna Olapoju Olawuni acid, lamarin da kona shi ba kadan ba.
Dan sandan mai gabatar da kara, ASP Abiodun Fagboyinbo, ya sanar da kotun cewa, Adetoro ta aikata laifin a ranar 12 ga watan Satumban 2017 wurin karfe 1 na dare a yankin Prime da ke Osogbo.
Bayan yin aika-aikar, Adetoro ta tsere inda daga bisani aka damketa a ranar Litinin.
Fagboyinbo ya sanar da kotun cewa, Olawuni ya matukar shan wahala sakamakon kunar kuma ya kasance yana yawon asibiti a jihar Edo.
Baya ga nan, an yi masa aiki daban-daban a jikinsa amma har a halin yanzu bai warke ba. Duk da dan sandan bai bayyana abinda ya assasa rigima tsakanin ma'auratan ba, Daily Trust ta gano cewa mai kare kanta ta zargi mijinta da ajiye karuwa a waje bayan yana da aure.
Adetoro bata amsa dukkan laifukan da ake zarginta da su ba, amma lauyanta mai suna Okobe Najite ya mika bukatar karbar belin wacce yake karewa.
Amma, Fagboyinbo ya soki wannan bukatar inda ya ja kunnen cewa wacce ake zargin za ta iya tsallake sharuddan belin.
Alkalin kotun, Abayomi Ajala, ya bukaci a tsare masa Adetoro a gidan gyaran hali da ke Ilesa har zuwa ranar Talata, 8 ga watan Satumba don ci gaba da shari'ar.
SOURCE: LEGIT.NG
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
SAYI KWAKWKWARAR DATAR MTN MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A SHAFUKAN
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Zargin neman mata: Matar aure ta wanke mijinta da acid, alkali ya daureta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?